Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 18:15-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.

16. Sai ka fanshe su suna 'yan wata ɗaya a bakin shekel biyar biyar, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

17. Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji.

18. Naman kuwa zai zama naka, duk da ƙirji na kaɗawa da cinyar dama da aka miƙa su hadaya ta kaɗawa.

19. “Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra'ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da 'ya'yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.”

20. Ubangiji kuma ya ce wa Haruna, “Ba za ka gāji kome a ƙasar Isra'ilawa ba, ba ka da wani rabo a cikinta. Ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra'ilawa.”

21. Ubangiji ya ce, “Na ba Lawiyawa kowace zaka ta Isra'ilawa gādo saboda aikinsu da suke ya a alfarwa ta sujada.

22. Nan gaba kada Isra'ilawa su zo kusa da alfarwa ta sujada don kada su yi zunubi, su mutu.

23. Gama Lawiyawa ne kaɗai za su yi aikin alfarwa ta sujada, wannan alhakinsu ne. Wajibi ne kuma ga zuriyarsu a kowane lokaci. Lawiyawa ba su da gādo tare da Isra'ilawa.

24. Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra'ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra'ilawa.”

25. Ubangiji ya ce wa Musa,

26. “Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa'ad da suka karɓi zaka daga Isra'ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa.

Karanta cikakken babi L. Kid 18