Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 11:19-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ba ma don kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko ashirin kaɗai za su ci ba.

20. Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa , suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”

21. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutum dubu ɗari shida (600,000) ne suke tafe tare da ni, ga shi kuwa, ka ce za ka ba su nama, za su ci har wata guda cur.

22. Za a yanyanka musu garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu, don su ishe su? Ko kuwa za a tattara musu dukan kifayen teku don su ishe su?”

23. Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”

24. Musa kuwa ya fita, ya faɗa wa jama'a maganar Ubangiji, ya kuma tattara dattawa saba'in daga cikin jama'ar, ya sa su tsaya kewaye da alfarwar.

25. Sa'an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba'in. Sa'ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba.

26. Akwai mutum biyu da suka ragu a zangon, sunan ɗayan Eldad, ɗayan kuwa Medad. Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon.

27. Sai wani saurayi ya sheƙa a guje ya faɗa wa Musa, ya ce, “Ga Eldad da Medad suna nan suna annabci a cikin zangon.”

28. Joshuwa ɗan Nun, mai yi wa Musa barantaka, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun, ya ce, “Ya shugabana, Musa, ka hana su.”

Karanta cikakken babi L. Kid 11