Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 10:20-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Shugaban rundunar kabilar mutanen Gad Eliyasaf ne, ɗan Deyuwel.

21. Daga nan sai Kohatawa masu ɗauke da kayayyaki masu tsarki suka tashi. Kafin su isa masaukin, an riga an kafa alfarwar.

22. Tutar zangon mutanen Ifraimu ta tashi, ƙungiyoyinsu na biye. Shugaban rundunarsu Elishama ne, ɗan Ammihud.

23. Shugaban rundunar kabilar mutanen Manassa Gamaliyel ne, ɗan Fedazur.

24. Shugaban rundunar kabilar mutanen Biliyaminu Abidan ne, ɗan Gideyoni.

25. A ƙarshe sai ƙungiyar mutanen Dan da take bayan dukan zangon, ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Ahiyezer ne, ɗan Ammishaddai.

26. Shugaban rundunar kabilar mutanen Ashiru Fagiyel ne, ɗan Okran.

27. Shugaban rundunar kabilar mutanen Naftali Ahira ne, ɗan Enan.

28. Wannan shi ne tsarin tafiyar Isra'ilawa bisa ga rundunansu sa'ad da sukan tashi.

29. Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamadayane, surukinsa, “Muna kan hanya zuwa wurin da Ubangiji ya ce zai ba mu, ka zo tare da mu, za mu yi maka alheri, gama Ubangiji ya alkawarta zai yi wa Isra'ila alheri.”

30. Amma ya ce masa, “Ba zan tafi ba, zan koma ƙasata da wurin dangina.”

31. Musa kuwa ya ce masa, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu, gama ka san jejin da muke zango, kai za ka zama idonmu.

32. Idan ka tafi tare da mu, kowane irin alheri da Ubangiji zai yi mana, mu kuma haka za mu yi maka.”

Karanta cikakken babi L. Kid 10