Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 9:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.”

5. Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama'a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji.

6. Musa kuma ya ce, “Ubangiji ya umarce ku ku yi dukan wannan, domin ɗaukakar Ubangiji za ta bayyana gare ku.”

7. Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama'a. Ka kuma kawo hadayar jama'a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

8. Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa.

9. 'Ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa a cikin jinin, ya shafa a zankayen bagaden, ya kuma zuba jinin a gindin bagaden.

10. Amma kitsen, da ƙodojin, da kitsen da yake rufe da hanta na hadaya don zunubi, ya ƙone su a bisa bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

11. Naman da fatar kuwa ya ƙone su a bayan zangon.

12. Haruna ya yanka hadaya ta ƙonawa, 'ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa a bagaden da kewayensa.

13. Suka kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa gunduwa tare da kan, sai ya ƙone su bisa bagaden.

14. Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa'an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden.

15. Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin.

Karanta cikakken babi L. Fir 9