Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 9:14-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa'an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden.

15. Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin.

16. Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa, ya yi kamar yadda aka faɗa.

17. Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗibi garin cike da tafin hannunsa, ya ƙone shi a bisa bagaden tare da hadaya ta ƙonawa ta safiya.

18. Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama'ar. 'Ya'yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.

19. Suka cire kitsen bijimin, da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji, da matsarmama.

20. Sai Haruna ya aza kitsen a bisa ƙirjin dabbobin ya ƙone kitsen a bisa bagaden.

21. Amma ya yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin da cinyoyi na dama ga Ubangiji, kamar yadda Musa ya umarta.

22. Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama'a, ya sa musu albarka sa'an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama.

23. Musa da Haruna suka shiga alfarwa ta sujada. Da suka fita, sai suka sa wa jama'a albarka. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana ga jama'a duka.

24. Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.

Karanta cikakken babi L. Fir 9