Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 6:15-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.

16. Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.

17. Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.

18. Kowane ɗa namiji cikin 'ya'yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka.

19. Sai Ubangiji ya ba Musa waɗannan ka'idodi,

20. domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice.

21. Za a shirya shi da mai a kwanon tuya. A kwaɓa shi sosai, a toya shi dunƙule dunƙule kamar hadaya ta gari, sa'an nan a kawo shi a miƙa shi don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

22. Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada.

23. Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.

Karanta cikakken babi L. Fir 6