Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.