Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 25:23-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.

24. “Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka.

25. Idan ɗan'uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan'uwansa ya jinginar.

26. Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa,

27. to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa'an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa.

28. Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa.

29. “Haka nan kuma idan mutum ya jinginar da gida a cikin birni mai garu, yana da izini ya fanshi abinsa a ƙarshen shekara guda.

30. Idan kuwa bai fanshi gidan a ƙarshen shekara guda ba, sai gidan nan da yake cikin birni mai garu ya zama mallakar wanda ya karɓi jinginar, da na zuriyarsa duka har abada. Ba za a mayar wa maigidan da gidan a shekara ta hamsin ta murna ba.

31. Amma gidajen da suke cikin ƙauyuka da ba su cikin garu, sai a lasafta su daidai da gonakin da suke cikin ƙasar, ana iya fansarsu, za a kuma mayar wa masu su a shekara ta hamsin ta murna.

Karanta cikakken babi L. Fir 25