Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 23:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji.

18. Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

19. Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama.

20. Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da 'yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist.

21. A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.

22. Sa'ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

23. Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

24. ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada.

25. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

26. Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

27. rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji.

28. Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu.

Karanta cikakken babi L. Fir 23