Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 23:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. A ranar da suka miƙa hadaya ta kaɗawa, za su kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.

13. Tare da wannan hadaya kuma, za su miƙa hadaya ta gari, humushi biyu na garwar gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Za su kuma miƙa hadaya ta sha da ruwan inabi kwalaba ɗaya.

14. Kada su ci sabon hatsin, wanda aka tuma, ko ɗanyensa, ko wanda aka yi gurasa da shi sai sun kawo hadayarsu ta sabon hatsi ga Allah. Za su kiyaye wannan ka'ida, da su da dukan zuriyarsu, har dukan zamanai masu zuwa.

15. Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji.

16. Kwana hamsin za su ƙirga zuwa kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa'an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji.

17. Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji.

18. Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Karanta cikakken babi L. Fir 23