Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 23:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ba Musa

2. waɗannan ka'idodi domin ƙayyadaddun idodi sa'a da Isra'ilawa za su taru domin yin sujada.

3. Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.

4. Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.

5. Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji.

6. Sa'an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai.

7. Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba.

8. A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.

Karanta cikakken babi L. Fir 23