Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 22:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya umarci Musa

2. ya faɗa wa Haruna, da shi da 'ya'yansa cewa, “Ku lura da tsarkakakkun abubuwa waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, don kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Ni ne Ubangiji.

3. Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji.

4. “Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,

5. da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,

6. duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna.

7. To, sa'ad da rana ta faɗi mutumin zai tsarkaka, bayan wannan ya iya cin tsarkakakkun abubuwan nan, gama ko dā ma abincinsa ne.

8. Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.

9. “Domin haka sai su kiyaye umarnaina don kada su yi zunubi su mutu ta wurin karya tsarkakakkun ka'idodina. Ni ne Ubangiji, ni na sa su tsarkaka.

10. “Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake zama tare da su ne, ko kuwa an ɗauke shi yana yi musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.

11. Amma idan firist ya sayi bawa da kuɗinsa, bawan ya zama dukiyarsa, bawan zai iya ci, haifaffun gidansa kuma za su iya cin tsattsarkan abincin.

12. Idan kuwa 'yar firist ta auri wani wanda ba firist ba, to, kada ta ci daga cikin tsarkakakkun hadayu.

13. Amma idan 'yar firist ɗin gwauruwa ce, ko sakakkiya, ba ta kuma da ɗa, ta kuwa koma gidan mahaifinta, sai ta ci daga cikin abincin mahaifinta kamar cikin kwanakin ƙuruciyarta. Amma wani dabam ba zai ci ba.

14. “Idan kuwa har wani mutum dabam ya ci daga cikin tsarkakakken abin ba da saninsa ba, to, sai ya maido abin ga firist, da ƙarin humushin tamanin abin.

15. Firist ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun abubuwan nan da jama'ar Isra'ila suke miƙawa ba,

16. da zai bar mutumin da bai cancanta ya ci ba, wannan zai jawo masa hukunci. Ni ne Ubangiji. Ni na tsarkake hadayun.”

17. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

Karanta cikakken babi L. Fir 22