Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 19:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa

2. ya faɗa wa dukan taron jama'ar Isra'ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne.

3. Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.

4. “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

5. “Sa'ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku.

6. A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta,

7. gama ta zama abar ƙyama, idan aka ci ta a rana ta uku, ba za ta zama abar karɓa ba.

8. Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama'a.

9. “Sa'ad da kuke girbin amfanin ƙasarku, kada ku girbe gefen gonakinku, kada kuma ku yi kala bayan da kuka gama girbi.

10. Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara 'ya'yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku.

Karanta cikakken babi L. Fir 19