Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 15:1-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi

2. domin jama'ar Isra'ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al'aurarsa, ƙazantacce ne.

3. Ko al'aurar tana ɗiga ko ta daina shi dai ƙazantacce ne.

4. Kowane gado da mai ɗigan ya kwanta a kai ya ƙazantu, da kowane abu da ya zauna a kai ya ƙazantu.

5. Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

6. Duk wanda kuma ya zauna a kan kowane abin da mai ɗigar ya zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

7. Wanda kuma ya taɓa jikin mai ɗigar, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

8. Idan mai ɗigar ya tofar da yau a kan wanda yake da tsabta, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

9. Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu.

10. Duk wanda ya taɓa kowane abin da yake ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har maraice, duk kuma wanda ya ɗauki wannan abu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

11. Duk wanda kuma mai ɗigar ya taɓa da hannunsa da bai wanke ba, sai wanda aka taɓa ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

12. Kaskon da mai ɗigar ya taɓa, sai a fasa shi, amma idan akushi ne sai a wanke shi da ruwa.

13. Sa'ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka.

14. A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.

15. Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.

16. Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

17. Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

Karanta cikakken babi L. Fir 15