Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 14:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa'an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura.

8. Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai.

9. A kan rana ta bakwai zai aske dukan gashin kansa, da gemunsa, da gashin girarsa, da duk gashin jikinsa. Sai kuma ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka.

10. A rana ta takwas zai kawo 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai.

11. Firist ɗin da zai tsarkake mutumin zai kawo wanda za a tsarkake da waɗannan abubuwa a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

12. Firist ɗin zai ɗauki ɗan rago ɗaya ya miƙa shi hadaya don diyyar laifi, da rabin moɗa na mai, ya miƙa su don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

13. Sa'an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki.

14. Firist zai ɗibi jinin hadaya don laifi ya shafa a leɓatun kunnen dama, da bisa babban yatsan hannun dama, da na ƙafar dama na wanda za a tsarkake ɗin.

15. Firist kuwa zai ɗibi man, ya zuba shi a tafin hannunsa na hagu.

16. Ya kuma tsoma yatsan hannunsa na dama a cikin man da yake a tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa man da yatsansa sau bakwai a gaban Ubangiji.

Karanta cikakken babi L. Fir 14