Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 13:23-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma idan tabon ya tsaya wuri ɗaya, bai bazu ba, tabon miki ke nan, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.

24. Ko kuma idan mutum ya ƙuna a fatar jiki, naman wurin ƙunar kuwa ya yi tabo jaja-jaja, da fari-fari, ko fari,

25. sai firist ya dudduba shi, in gashin wurin tabo ya zarce fatar, to, kuturta ce ta faso a cikin ƙunar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce.

26. Amma idan firist ya dudduba tabon, ya ga gashin tabon bai zama fari ba, zurfin tabon kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, firist zai kulle shi kwana bakwai.

27. A kan rana ta bakwai, zai sāke dubansa, idan tabon yana bazuwa cikin fatar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.

28. Amma idan tabon ya tsaya a wuri ɗaya, bai bazu a fatar jikin ba, ya kuma dushe, to, kumburi ne na ƙunar, firist zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, gama tabon ƙuna ne.

29. Sa'ad da mace ko namiji na da cuta a kai, ko a gemu,

30. sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne.

Karanta cikakken babi L. Fir 13