Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 13:2-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci.

3. Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne.

4. Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai.

5. A rana ta bakwai firist zai ƙara dudduba shi, in ya ga cutar ba ta yaɗu a fatar jikin mutumin ba, sai ya sāke kulle shi waɗansu kwana bakwai kuma.

6. A rana ta bakwai sai firist ya sāke dubansa, idan ciwon ya dushe, cutar kuma ba ta yaɗuwa a fatar jikin mutumin, firist zai hurta, cewa, mutumin tsattsarka ne, ɓamɓaroki ne kawai, sai ya wanke tufafinsa.

7. Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar jikin mutumin bayan da ya nuna kansa ga firist don tsarkakewa, sai ya sāke zuwa gaban firist.

8. Firist zai duba shi, idan ɓamɓaroki ya yaɗu a fatar, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba ɓamɓaroki ba ne, kuturta ce.

9. Sa'ad da cutar kuturta ta kama mutum, sai a kai shi wurin firist.

10. Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin,

11. to, kuturta ce da ta daɗe a fatar jikinsa. Firist kuwa zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba za a kulle shi ba, gama ya tabbata marar tsarki ne.

12. Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist,

13. firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka.

14. Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki.

Karanta cikakken babi L. Fir 13