Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 11:30-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

31. Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice.

32. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka.

33. Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon.

34. Kowane irin abincin da yake cikinsa kuma da yake da ruwa a cikinsa, zai haramtu. Kowane irin abin sha da yake cikinsa kuma, zai haramtu.

35. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai, zai haramtu, ko randa ce, ko murhu, sai a farfasa, sun ƙazantu, haram ne a gare ku.

36. Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu.

37. Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba.

38. Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku.

39. Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice.

40. Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.

41. Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba,

42. duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa.

43. Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa.

44. Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne.

45. Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.

46. Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu.

Karanta cikakken babi L. Fir 11