Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Dabbobin da yake Halal da na Haram

1. Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi

2. domin Isra'ilawa. Za ku ci kowace irin dabbar da take a duniya,

3. wadda take da rababben kofato, wadda kuma take yin tuƙa.

4. Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku.

5. Rema tana tuƙa, amma ba ta da rababben kofato, haram ce a gare ku.

6. Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku.

7. Alade yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, haram ne a gare ku.

8. Ba za ku ci namansu ba, ba kuwa za ku taɓa mushensu ba, gama haram ne a gare ku.

9. Kwa iya cin waɗannan abubuwan da suke cikin ruwa, kowane abin da yake da ƙege da kamɓorin da yake cikin tekuna ko koguna.

10. Amma kowace irin halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, abar ƙyama ce a gare ku.

11. Namansu kuma zai zama abin ƙyama a gare ku, ba za ku ci ba. Mushensu kuma abin ƙyama ne.

12. Kowane irin abin da yake cikin ruwa da ba shi da ƙege da kamɓori, abin ƙyama ne a gare ku.

13. Za ku ji ƙyamar waɗannan irin tsuntsaye, ba za ku ci su ba, gama abin ƙyama ne su, wato, gaggafa, da mikiya, da ungulun kwakwa,

14. da shirwa, da buga zabi, da irinsu,

15. da kowane irin hankaka,

16. da jimina, da mujiya, da shaho, da irinsu,

17. da ƙururu, da babba da jaka, da zarɓe,

18. da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu,

19. da shamuwa, da jinjimi da irinsa, da burtu, da jemage.

20. Dukan ƙwarin da yake da fikafikai ƙazantattu ne,

21. sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

22. Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu.

23. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, sun a kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.

24. Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har faɗuwar rana.

25. Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice.

26. Kowace dabba wadda ba ta da rababben kofato, ba ta kuma tuƙa, haram ce a gare ku. Duk wanda ya taɓa su zai ƙazantu.

27. Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice.

28. Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.

29. Waɗannan ƙananan dabbobin da suke rarrafe a ƙasa haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

30. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

31. Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice.

32. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa'an nan zai tsarkaka.

33. Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon.

34. Kowane irin abincin da yake cikinsa kuma da yake da ruwa a cikinsa, zai haramtu. Kowane irin abin sha da yake cikinsa kuma, zai haramtu.

35. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai, zai haramtu, ko randa ce, ko murhu, sai a farfasa, sun ƙazantu, haram ne a gare ku.

36. Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu.

37. Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba.

38. Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku.

39. Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice.

40. Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.

41. Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba,

42. duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa.

43. Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa.

44. Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne.

45. Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.

46. Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu.

47. Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.