Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 10:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. 'Ya'yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.

2. Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji.

3. Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma'anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama'ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit.

4. Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan 'ya'ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin 'yan'uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.”

5. Sai suka zo, suka kama rigunan matattun suka ɗauke su zuwa bayan zango kamar yadda Musa ya faɗa.

6. Musa kuma ya ce wa Haruna, da 'ya'yansa maza, wato, Ele'azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama'a duka, amma 'yan'uwanku, wato, dukan Isra'ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone.

7. Kada kuwa ku fita daga cikin alfarwa ta sujada don kada ku mutu, gama an shafa muku man keɓewa na Ubangiji.” Sai suka yi yadda Musa ya faɗa.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da Haruna ya ce,

9. “Kada kai da 'ya'yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa'ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku.

10. Sai ku bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki, da tsakanin abin da yake halal da abin da yake haram.

11. Ku kuma koya wa mutanen Isra'ila dukan dokokin da Ubangiji ya ba su ta hannun Musa.”

12. Musa kuwa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda suka ragu, wato, Ele'azara da Itamar, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji, ku ci ba tare da yisti ba a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.

13. Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni.

Karanta cikakken babi L. Fir 10