Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 28:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba shi da tsoro.

2. Al'umma za ta ƙarfafa ta jure idan shugabanninta masu basira ne, masu hankali. Amma idan ƙasar mai aikata zunubi ce za ta sami shugabanni da yawa.

3. Mai mulki wanda yake zaluntar talakawa, ya zama kamar ruwa mai lalatar da amfanin gona.

4. Wanda ba ya bin doka tare da mugaye yake, amma idan kana bin doka kai abokin gāban mugaye ne.

5. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai.

6. Gara ka zama matalauci mai aminci da ka zama mawadaci, marar aminci.

7. Saurayi wanda ya kiyaye doka mai basira ne shi, amma wanda yake abuta da 'yan iska zai zama mai jawo wa mahaifinsa kunya.

8. Idan kana tara dukiya ta wurin ba da bashi da ruwa kana kuma ƙwarar jama'a, dukiyarka za ta koma ga wanda yake yi wa talakawa alheri.

9. Idan ka ƙi biyayya ga doka, Allah zai ƙi jin addu'o'inka.

10. Idan ka yaudari mutumin kirki don ya faɗa cikin mugunta, kai kanka ne za ka fāɗa cikin tarkon da ka haƙa. Marar laifi kuwa zai sami babban sakamako.

11. Attajirai, a ko yaushe, zato suke su masu hikima ne, amma matalauci mai tunani ya fi sanin abin da yake daidai.

12. Sa'ad da mutanen kirki suke sarauta, kowa da kowa yakan yi biki, amma sa'ad da mugaye suka kama mulki mutane sukan riƙa ɓuya.

13. Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa'an nan Allah zai yi maka jinƙai.

14. Mutumin da yake tsoron Ubangiji ko yaushe, zai yi farin ciki, amma idan ya taurare zai lalace.

15. Talakawa ba su da wani taimako sa'ad da suke ƙarƙashin mulkin mugun. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanɗa.

Karanta cikakken babi K. Mag 28