Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 19:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin manyan mutane, kowa na so a ce shi abokin mutumin nan ne, mai yawan alheri.

7. 'Yan'uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Kome ƙoƙarin da zai yi ba zai sami ko ɗaya ba.

8. Ka yi wa kanka gatanci, ka koyi dukan abin da kake iyawa, sa'an nan ka tuna da abin da ka koya, za ka arzuta.

9. Ba wanda zai faɗi ƙarya a majalisa ya rasa shan hukunci, maƙaryaci, tasa ta ƙare.

10. Ko kusa wawaye ba za su yi zaman jin daɗi ba, haka nan kuma bayi ba za su yi mulki a kan iyayengijinsu ba.

11. Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba.

12. Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.

13. Dakikin ɗa yana jawo wa mahaifinsa lalacewa, mace mai mita tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

14. Mutum na iya cin gādon gida da kuɗi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kaɗai yake ba shi mace mai hankali.

Karanta cikakken babi K. Mag 19