Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 19:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Gara mutum ya zama matalauci amma mai aminci, da a ce ya zama maƙaryaci, wawa.

2. Yin ɗokin da ba ilimi ba shi da amfani, rashin haƙuri kuma zai jawo maka wahala.

3. Waɗansu mutane sukan lalatar da kansu ta wurin ayyukansu na jahilci, sa'an nan su sa wa Ubangiji laifi.

4. Attajirai sukan sami sababbin abokai a ko yaushe, amma matalauta ba zu su iya riƙon 'yan kaɗan da suke da su ba.

5. Idan ka faɗi ƙarya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kuɓuta ba.

6. Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin manyan mutane, kowa na so a ce shi abokin mutumin nan ne, mai yawan alheri.

7. 'Yan'uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Kome ƙoƙarin da zai yi ba zai sami ko ɗaya ba.

8. Ka yi wa kanka gatanci, ka koyi dukan abin da kake iyawa, sa'an nan ka tuna da abin da ka koya, za ka arzuta.

Karanta cikakken babi K. Mag 19