Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 14:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.

9. Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.

10. Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.

11. Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.

12. Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.

13. Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa'ad da murna ta tafi, ko yaushe baƙin ciki yana nan.

14. Mugu zai sami abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai sami sakayyar ayyukansa.

15. Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la'akari yana lura da takawarsa.

16. Mutum mai hankali yana lura don ya kauce wa wahala, amma wawa rashin kula gare shi, yakan aikata kome da gaggawa.

17. Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.

18. Jahilai sukan sami abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci.

19. Tilas mugaye su rusuna wa adalai, su roƙe su tagomashi da tawali'u.

20. Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa.

Karanta cikakken babi K. Mag 14