Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 6:5-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.”

6. Joshuwa ɗan Nun kuwa ya kirawo firistoci, ya ce musu, “Ɗauki akwatin alkawarin, sa'an nan firistoci bakwai su ɗauki ƙaho bakwai na raguna su wuce a gaban akwatin alkawarin Ubangiji.”

7. Ya kuma ce wa jama'a, “Ku wuce, ku zaga birnin, masu makamai kuma su wuce a gaban akwatin Ubangiji.”

8. Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama'a, firistoci bakwai waɗanda suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su.

9. Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, 'yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni.

10. Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, “Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa'an nan za ku yi ihu.”

11. Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa'an nan suka koma zango, suka kwana.

12. Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji.

13. Firistoci bakwai ɗin da suke riƙe da ƙahoni bakwai na raguna, suka wuce gaban akwatin Ubangiji suna ta busawa, masu makamai suna tafe a gabansu, 'yan tsaron baya suna biye da akwatin Ubangiji, ana ta busa ƙahoni.

14. A rana ta biyu kuma suka zaga birnin sau ɗaya, sa'an nan suka koma zango. Haka suka yi ta yi har kwana shida.

15. A rana ta bakwai kuwa suka tashi da sassafe, suka yi sammako, suka zaga birnin yadda suka saba yi har sau bakwai. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai.

16. A zagawa ta bakwai, sa'ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin.

17. Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.

18. Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa.

19. Amma dukan azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe keɓaɓɓu ne ga Ubangiji. Za a shigar da su cikin taskar masujadar Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Josh 6