Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 3:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.

2. Bayan kwana uku sai shugabannin jama'a suka bibiya zango,

3. suna umartar jama'ar suna cewa, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi,

4. domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.”

5. Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku.”

6. Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama'ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama'a.

7. Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai.

8. Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ”

9. Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.”

10. Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.

Karanta cikakken babi Josh 3