Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 22:26-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Don haka muka ce, ‘Bari mu gina bagade, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba,

27. amma domin ya zama shaida tsakaninmu da ku, da tsakanin zuriyarmu da taku, don mu ci gaba da bautar Ubangiji da hadayunmu na ƙonawa, da na sadaka, da na salama.’ 'Ya'yanku kuma ba za su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’

28. Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’

29. Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”

30. Sa'ad da Finehas, firist, da shugabannin jama'a, wato shugabannin iyalan Isra'ila, suka ji maganar da Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai.

31. Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.”

32. Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, da shugabannin suka komo daga wurin Ra'ubainawa da Gadawa a ƙasar Gileyad, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mutanen Isra'ila, suka ba su rahoton abin da suka ji.

33. Mutanen Isra'ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra'ubainawa da Gadawa suke zaune ba.

34. Ra'ubainawa da Gadawa suka sa wa bagaden suna Shaida, domin in ji su, “Shi shaida ne a tsakaninmu, cewa Ubangiji shi ne Allah.”

Karanta cikakken babi Josh 22