Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 22:24-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Saboda gudun gaba ne muka yi haka, domin kada wata rana 'ya'yanku su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ruwanku da Ubangiji, Allah na Isra'ila.

25. Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra'ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ To, da haka 'ya'yanku su hana 'ya'yanmu yi wa Ubangiji sujada.

26. Don haka muka ce, ‘Bari mu gina bagade, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba,

27. amma domin ya zama shaida tsakaninmu da ku, da tsakanin zuriyarmu da taku, don mu ci gaba da bautar Ubangiji da hadayunmu na ƙonawa, da na sadaka, da na salama.’ 'Ya'yanku kuma ba za su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’

28. Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’

29. Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”

30. Sa'ad da Finehas, firist, da shugabannin jama'a, wato shugabannin iyalan Isra'ila, suka ji maganar da Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai.

31. Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.”

32. Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, da shugabannin suka komo daga wurin Ra'ubainawa da Gadawa a ƙasar Gileyad, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mutanen Isra'ila, suka ba su rahoton abin da suka ji.

Karanta cikakken babi Josh 22