Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 22:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan Joshuwa ya kira mutanen kabilar Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa.

2. Ya ce musu, “Kun aikata dukan abin da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku, kun kuma yi biyayya da dukan abin da na umarce ku.

3. Ba ku yar da 'yan'uwanku dukan waɗannan yawan kwanaki, har wa yau ba. Amma kuka kiyaye umarnin Ubangiji Allahnku sosai.

4. Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba 'yan'uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun.

5. Sai dai ku kiyaye umarnai da dokokin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa, ku kiyaye dokokinsa, ku manne masa, ku bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku.”

6. To, Joshuwa ya sa musu albarka, sa'an nan ya sallame su, suka koma gida.

7. Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka,

8. ya ce musu, “Ku koma gidajenku da wadata mai yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa, da zinariya, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da tufafi masu yawa. Ku raba da 'yan'uwanku ganimar da kuka kwaso daga abokan gabanku.”

9. Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka koma gida. Suka yi bankwana da sauran 'yan'uwansu Isra'ilawa a Shilo ta ƙasar Kan'ana. Suka koma ƙasar Gileyad, ƙasar da suka gāda bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Musa.

10. Sa'ad da suka kai Gelilot, kusa da Urdun, a gefen da yake wajen ƙasar Kan'ana, suka gina babban bagade a wurin.

11. Sauran Isra'ilawa kuwa suka ji labari cewa, “Ga shi, Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa sun gina bagade a Gelilot a kan iyakar ƙasar Kan'ana, a wajen hayinsu na yammacin Urdun.”

12. Da Isra'ilawa suka ji haka sai dukansu suka tattaru a Shilo don su kai musu yaƙi.

13. Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.

14. Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra'ila.

15. Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu,

16. “In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade.

Karanta cikakken babi Josh 22