Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 21:7-23-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna.

8. Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.

9. Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata.

10. Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko.

11. Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak.

12. Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.

13. Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata,

14. da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata,

15. da Holon tare da wuraren kiwo nata, da Debir tare da wuraren kiwo nata,

16. da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu.

17. Daga cikin kabilar Biliyaminu aka ba su birane huɗu, wato Gibeyon tare da wuraren kiwo nata, da Geba tare da wuraren kiwo nata,

18. da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata.

19. Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu.

20-22. Aka ba sauran Kohatiyawa na iyalan Lawiyawa birane huɗu daga kabilar Ifraimu. Aka ba su Shekem tare da wuraren kiwo nata, a ƙasar tuddai ta Ifraimu, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Gezer tare da wuraren kiwo nata, da Yokmeyam tare da wuraren kiwo nata, da Bet-horon tare da wuraren kiwo nata.

23-24. Aka kuma ba su birane huɗu daga kabilar Dan, wato Elteki tare da wuraren kiwo nata, da Gibbeton tare da wuraren kiwo nata, da Ayalon tare da wuraren kiwo nata, da Gat-rimmon tare da wuraren kiwo nata.

Karanta cikakken babi Josh 21