Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 21:18-34-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata.

19. Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu.

20-22. Aka ba sauran Kohatiyawa na iyalan Lawiyawa birane huɗu daga kabilar Ifraimu. Aka ba su Shekem tare da wuraren kiwo nata, a ƙasar tuddai ta Ifraimu, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Gezer tare da wuraren kiwo nata, da Yokmeyam tare da wuraren kiwo nata, da Bet-horon tare da wuraren kiwo nata.

23-24. Aka kuma ba su birane huɗu daga kabilar Dan, wato Elteki tare da wuraren kiwo nata, da Gibbeton tare da wuraren kiwo nata, da Ayalon tare da wuraren kiwo nata, da Gat-rimmon tare da wuraren kiwo nata.

25. Daga cikin rabin kabilar Manassa, aka ba su birane biyu, su ne Ta'anak tare da wuraren kiwo nata, da Bileyam tare da wuraren kiwo nata.

26. Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba sauran Kohatawa na iyalan Lawiyawa guda goma ne.

27. Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata.

28-29. Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin kabilar Issaka, biranen su ne, Kishiyon da wuraren kiwo nata, da Daberat da wuraren kiwo nata, da Yarmut da wuraren kiwo nata, da Enganim da wuraren kiwo nata.

30-31. Daga cikin rabon kabilar Ashiru aka ba su birane huɗu, su ne Mishal da wuraren kiwo nata, da Abdon da wuraren kiwo nata, da Helkat da wuraren kiwo nata, da Rehob da wuraren kiwo nata.

32. Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata.

33. Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba iyalan Gershonawa guda goma sha uku ne.

34-35. Aka ba iyalan Merari na cikin Lawiyawa birane huɗu daga cikin rabon kabilar Zabaluna. Biranen ke nan, Yakneyam da wuraren kiwo nata, da Karta da wuraren kiwo nata, da Rimmon da wuraren kiwo nata, da Nahalal da wuraren kiwo nata.

Karanta cikakken babi Josh 21