Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 19:40-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Kuri'a ta bakwai ta faɗo a kan kabilar Dan bisa ga iyalanta.

41. Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh,

42. da Shalim, da Ayalon, da Itla,

43. da Elon, da Timna, da Ekron,

44. da Elteki, da Gebbeton, da Ba'alat,

45. da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon,

46. da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa.

47. Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan.

48. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.

49. Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu.

50. Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki.

51. Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama'ar Isra'ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri'a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.

Karanta cikakken babi Josh 19