Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 17:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Aka ba kabilar Manassa, ɗan farin Yusufu, nata rabon gādo. Makir ɗan farin Manassa, uban Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan domin shi jarumi ne.

2. Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manassa nasu rabon gādo bisa ga iyalansu, wato Abiyezer, da Helek, da Asriyel, da Shekem, da Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne 'ya'yan Manassa, maza, bisa ga iyalansu.

3. Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da 'ya'ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

4. Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji.

5. Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun,

6. domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad.

7. Yankin ƙasar Manassa ya kai daga Ashiru zuwa Mikmetat wadda take gabas da Shekem. Iyakar kuma ta miƙa kudu zuwa mazaunan En-taffuwa.

8. Ƙasar Taffuwa tana hannun mutanen Manassa, amma mutanen Ifraimu ne suke da garin Taffuwa wanda yake iyakar yankin Manassa.

9. Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum.

10. Ƙasar wajen kudu ta Ifraimu ce, ta wajen arewa kuwa ta Manassa. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Mutanen Ashiru suna wajen arewa, mutanen Issaka kuwa wajen gabas.

Karanta cikakken babi Josh 17