Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 16:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel.

2. Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa'an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa.

3. Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa'an nan ya gangara a teku.

4. A nan ne jama'ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo.

5. Karkarar jama'ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu.

6. Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta'anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa.

Karanta cikakken babi Josh 16