Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 12:7-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba'al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra'ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu,

8. da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9. Sunayen sarakunan su ne, Sarkin Yariko, da Sarkin Ai, da yake kusa da Betel,

10. da Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron,

11. da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish,

12. da Sarkin Eglon, da Sarkin Gezer,

13. da Sarkin Debir, da Sarkin Geder,

14. da Sarkin Horma, da Sarkin Arad,

15. da Sarkin Libna, da Sarkin Adullam,

16. da Sarkin Makkeda, da Sarkin Betel,

17. da Sarkin Taffuwa, da Sarkin Hefer,

18. da Sarkin Afek, da Sarkin Lasharon,

19. da Sarkin Madon, da Sarkin Hazor,

20. da Sarkin Shimron-meron, da Sarkin Akshaf,

21. da Sarkin Ta'anak, da Sarkin Magiddo,

Karanta cikakken babi Josh 12