Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 1:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki,

2. “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa.

3. Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa.

4. Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku.

5. Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba.

6. Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu.

7. Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da haka nan za ka arzuta cikin dukan harkokinka.

8. Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.

9. Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”

10. Sai Joshuwa ya umarci shugabannin jama'a, ya ce,

11. “Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”

12. Joshuwa kuma ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa,

13. “Ku tuna da maganar da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku da ita, ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai hutar da ku, zai kuma ba ku wannan ƙasa.’

14. Da matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobinku, za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a wannan hayin Urdun, amma jarumawanku su haye tare da 'yan'uwanku da shirin yaƙi domin su taimake su,

Karanta cikakken babi Josh 1