Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 9:17-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

18. Muguntar jama'a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta take murtukewa har sama.

19. Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko'ina a ƙasar, yana hallakar da jama'a, kowa na ta kansa.

20. A ko'ina a ƙasar jama'a sukan wawashe su ci ɗan abincin da suke iya samu, amma ba su taɓa ƙoshi ba. Har 'ya'yansu ma suke ci!

21. Jama'ar Manassa da jama'ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

Karanta cikakken babi Ish 9