Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 9:12-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra'ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

13. Jama'ar Isra'ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba.

14. A rana ɗaya Ubangiji zai hukunta shugabannin Isra'ila da jama'arta. Zai hallaka kawunansu da ƙafafunsu, da dabino da iwa,

15. wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi!

16. Su waɗanda suke bi da jama'an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.

17. Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

18. Muguntar jama'a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta take murtukewa har sama.

19. Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko'ina a ƙasar, yana hallakar da jama'a, kowa na ta kansa.

Karanta cikakken babi Ish 9