Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 65:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum.

18. Ku yi murna da farin ciki a kan abin da na halitta. Sabuwar Urushalima da nake halittawa za ta cika da murna, jama'arta kuma za su yi farin ciki.

19. Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama'arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.

20. Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.

21-22. Mutane za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba. Mutanena za su yi tsawon rai kamar itatuwa. Za su ci cikakkiyar moriyar abubuwan da suka yi aikinsu.

23. Aikin da suka yi zai yi nasara, 'ya'yansu ba za su gamu da bala'i ba, zan sa musu albarka duk da zuriyarsu har dukan zamanai.

24. Zan amsa addu'o'insu tun ma kafin su gama yin addu'a gare ni.

25. Kyarketai da 'yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci budu kamar yadda shanu suke yi. Maciji ba zai ƙara zama abu mai hatsari ba. A kan Sihiyona tsattsarkan dutsena, ba za a sami wani abu da zai cutar ba, ko wani mugun abu.”

Karanta cikakken babi Ish 65