Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 62:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya Urushalima, na sa matsara a garukankiBa za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa,Ba kuwa za su bari ya manta ba!

7. Ba za su bari ya huta ba, sai ya ceci Urushalima tukuna,Ya sa ta zama birnin da dukan duniya za ta yaba wa.

8. Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi,Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi.“Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba,Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.

9. Amma ku da kuka shuka hatsin kuka kuma girbe shi,Za ku ci abinci, ku yi yabon Ubangiji!Ku da kuka lura da itatuwan inabi kuka tara su,Za ku sha ruwan inabi a filayen Haikalina.”

10. Ku mutanen Urushalima, ku fita daga cikin birni,Ku gyara hanyoyi domin jama'arku da suke komowa!Ku shirya babbar hanya,Ku kawar da duwatsu daga hanyar!Ku sa alama domin al'ummai su sani,

11. Ubangiji yana sanarwa ga dukan duniya,Cewa, “Ku ce wa jama'ar Urushalima,Ubangiji Mai Cetonku yana zuwa,Yana kawo mutanen da ya cece su.”

12. Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama'ar Allah,”“Jama'ar da Ubangiji ya Fansa!”Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,”“Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”

Karanta cikakken babi Ish 62