Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 6:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sa'an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”

11. Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?”Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.

12. Zan sa jama'a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango.

13. Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.”Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama'ar Allah zuwa gaba.

Karanta cikakken babi Ish 6