Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 6:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.

2. Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi.

3. Suna ta kiran junansu suna cewa,“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki!Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne!Ɗaukakarsa ta cika duniya.”

4. Amon muryoyinsu ya sa harsashin ginin Haikali ya girgiɗa, Haikalin kansa kuma ya game da hayaƙi.

5. Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”

6. Sa'an nan ɗaya daga cikin talikan ya tashi ya sauko zuwa gare ni, yana riƙe da garwashin wuta wanda ya ɗauko da arautaki daga bagade.

7. Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”

8. Sai na ji Ubangiji yana cewa, “Wa zan aika? Wa zai zama manzonmu?”Sai na amsa na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

9. Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”

Karanta cikakken babi Ish 6