Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 58:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Irin azumin da nake so ke nan ne? Wato ranar da mutum zai ƙasƙantar da kansa kawai. Wato ku sunkuyar da kanku ne kamar jema, ku kuma shimfiɗa tsumma, ku barbaɗa toka a inda kuke zama. Kun iya ce da wannan azumi, karɓaɓɓiyar rana ga Ubangiji?

6. “To, ba irin wannan azumi ne na zaɓa ba? Wato ku kwance sarƙoƙin mugunta, ku kwance masu karkiya, ku 'yantar da waɗanda ake zalunta, ku kakkarye kowace karkiya.

7. Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.

8. “Sa'an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, za ku warke nan da nan. Adalcinku zai yi muku jagora, zatina zai rufa muku baya.

9. Sa'an nan za ku yi kira, ni kuwa zan amsa, za ku yi kuka, ni kuwa zan ce muku, ‘Ga ni.’“Idan kuka kawar da karkiya daga cikinku, kuka daina nuna wa juna yatsa, da faɗar mugayen maganganu,

10. idan kuka ƙosar da mayunwata, kuka biya bukatar waɗanda suke shan tsanani, sa'an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu, duhunku kuma zai zama kamar hasken tsakar rana.

11. Zan bi da ku kullayaumin, zan biya bukatarku da abubuwa masu kyau, in sa ƙasusuwanku su yi ƙarfi, ku zama kamar lambun da ake masa banruwa, za ku zama kamar maɓuɓɓugar ruwa da ba ta ƙonewa.

12. Za ku sāke gina tsofaffin kufanku na dā can, za ku sāke kafa tushen zuriya da yawa. Za a kira ku, ‘Masu gyaran abin da ya lalace, masu sāke gyaran gidaje.’ ”

13. Ubangiji ya ce, “Idan kun juyo kuna kiyaye ranar Asabar, kuka daina annashuwarku a tsattsarkar ranata, kuka kuma kira Asabar ranar murna, tsattsarkar rana ta Ubangiji, mai daraja, idan kun girmama ta, har kuka daina bin son zuciyarku, ba ku kuma bar shagulgula su ɗauke hankalinku ba, ko ku hurta maganganun banza,

14. sa'an nan ne za ku yi murna cikin Ubangiji, zan sa ku a kan maɗaukakan wurare na duniya. Zan kuma ciyar da ku da gādon mahaifinku Yakubu, ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ish 58