Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 50:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Kuna tsammani na kori mutanenaKamar yadda mutum yakan saki mata tasa?To, in haka ne ina takardar kisan auren?Kuna tsammani na sayar da ku cikin bautaKamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa?A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku,Aka tafi da ku saboda da laifofinku.

2. “Don me mutanena ba su amsa baSa'ad da na je wurinsu domin in cece su?Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu?Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne?Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina,Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada,Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.

3. Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu,In sa ya zama makoki domin matattu.”

4. Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa,Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi.A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini.

5. Ubangiji ya ba ni fahimi,Ban kuwa yi masa tayarwa baKo in juya in rabu da shi.

6. Na tsiraita ga masu dūkana.Ban hana su sa'ad da suke zagina ba,Suna tsittsige gemuna,Suna tofa yau a fuskata.

7. Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba,Gama Ubangiji Allah yana taimakona.Na ƙarfafa kaina domin in jure da su.Na sani ba zan kunyata ba,

Karanta cikakken babi Ish 50