Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 5:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna,Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa.Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau,Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai!Ya zaci za su aikata abin da yake daidai,Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!

8. Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.

9. Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.

10. Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”

11. Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa.

12. A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.

13. Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.

14. Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama'a masu hayaniya.

15. Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su.

16. Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa.

17. A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.

Karanta cikakken babi Ish 5