Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 49:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Mutanena za su zo daga can nesa,Daga Birnin Sin a kudu,Daga yamma, da arewa.”

13. Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya!Bari duwatsu su ɓarke da waƙa!Ubangiji zai ta'azantar da mutanensa,Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.

14. Amma mutanen Urushalima suka ce,“Ubangiji ya yashe mu!Ya manta da mu.”

15. Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce,“Mace za ta iya mantawa da jaririnta,Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa?Ya yiwu mace ta manta da ɗanta,To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.

16. Ya Urushalima, ba zan taɓa mantawa da ke ba,Na rubuta sunanki a gabana.

17. “Su waɗanda za su sāke gina ki suna tafe yanzu,Waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su tashi.

18. Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa!Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida!Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai,Za ki yi fāriya da mutanenki,Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta!

19. “Aka lalatar da ƙasar, ta zama kufai,Amma yanzu za ta yi wa waɗanda suke komowa domin su zauna cikinta kaɗan.Waɗanda suka lalatar da ke kuwa,Za a kawar da su daga gare ki.

20. Mutanenki da aka haifa a lokacin zaman talala,Wata rana za su ce miki,‘Wannan ƙasa ta yi kaɗan ƙwarai,Muna bukatar ƙarin wurin zama!’

21. Sa'an nan za ki ce wa kanki,‘Wa ya haifa mini waɗannan 'ya'ya?Na rasa 'ya'yana, ba kuwa zan iya haifar waɗansu ba.Aka kore ni, aka yi mini ɗaurin talala,Wane ne ya haifi waɗannan 'ya'ya?Aka bar ni, ni kaɗai,Daga ina waɗannan 'ya'ya suka fito?’ ”

22. Ubangiji Allah ya ce wa jama'arsa,“Zan nuna alama ga al'ummai,Za su kuwa kawo 'ya'yanku gida.

23. Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku,Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye.Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma,Da tawali'u za su nuna muku bangirma.Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji,Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”

24. Kuna iya ku ƙwace wa sojoji wason da suka yi?Kuna iya kuɓutar da 'yan kurkuku daga ɗaurin masu baƙin mulki?

25. Ubangiji ya amsa ya ce,“Wannan shi ne ainihin abin da zai faru.Za a ƙwace kamammun yaƙi,Za a kuma ƙwace wason da masu baƙin mulki ya yi.Zan yi yaƙi da dukan wanda yake yaƙi da ku,Zan kuwa kuɓutar da 'ya'yanku.

26. Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna,Za su yi māye, da kisankai, da fushi.Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji,Wanda ya cece ku, ya fanshe ku.Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.”

Karanta cikakken babi Ish 49