Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 48:14-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. “Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne!Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba,Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila,Zai yi abin da na umarce shi.

15. Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi,Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.

16. “Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni,Ku ji abin da nake faɗa.Tun da farko na yi magana da ku a fili,A koyaushe nakan cika maganata.”(Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)

17. Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce,“Ni ne Ubangiji Allahnku,Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku,Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.

18. “Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum!Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominkuKamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba!Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwaDa suke bugowa zuwa gāɓa.

19. Zuriyarku za su yi yawa kamar tsabar yashi,Zan kuma tabbatar, cewa ba za a hallaka su ba.”

20. Ku fita daga Babila, ku tafi a sake!Ku yi sowar albishir da farin ciki, ku sa a sani a ko'ina,“Ubangiji ya fanshi bawansa Isra'ila!”

21. Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi,Ba su sha wahalar ƙishi ba.Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu,Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.

22. Ubangiji ya ce, “Ba mafaka domin masu zunubi.”

Karanta cikakken babi Ish 48