Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 47:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amma ba da jimawa ba, a rana ɗayaDukan waɗannan al'amura za su faru.Kome sihirin da za ki yi,Za ki rasa 'ya'yanki, ki kuwa zama gwauruwa.

10. “Kin amince da kanki cikin muguntarki,Kina tsammani ba wanda yake ganinki.Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata,Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah,Ba mai kama da ni!’

11. Duk da haka bala'i zai auko miki,Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba,Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya,Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!

12. Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki,Kina amfani da su tun kina ƙarama.Watakila za su yi miki wani taimako,Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.

13. Kome shawarar da kika samu ba ki da ƙarfi.Bari mashawartanki su fito su cece ki,Waɗancan mutane masu binciken taurariWaɗanda suka zana taswirar sammai,Su kuma faɗa mikiDukan abin da zai faru da yake wata wata.

14. “Za su zama kamar budu,Wuta kuwa za ta ƙone su ƙurmus!Ba ma za su ko iya ceton kansu ba.Harshen wuta zai fi ƙarfinsu,Ba wutar da za su zauna, su ji ɗumi!

15. Nan ne inda shawararsu za ta kai ki,Waɗannan masanan taurari da kika yi ta neman shawararsu dukan kwanakin ranki.Dukansu za su bar ki, kowa ya tafi inda ya nufa,Ba wanda zai ragu da zai cece ki.”

Karanta cikakken babi Ish 47