Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 45:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji!Ubangiji ya sa shi ya ci al'ummai,Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna,Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni.Ubangiji ya ce wa Sairus,

2. “Ni kaina zan shirya hanya dominka,Ina baji duwatsu da tuddai.Zan kakkarye ƙyamaren tagulla,In kuma daddatse gagara badau na baƙin ƙarfe.

3. Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare,Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji,Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.

4. Na sa ka domin ka taimaki bawana Isra'ila,Jama'ar da ni na zaɓa.Na ba ka girma mai yawa,Ko da yake kai ba ka san ni ba.

5. “Ni ne Ubangiji, ba wani Allah sai ni.Zan ba ka irin ƙarfin da kake bukata,Ko da yake kai ba ka san ni ba.

6. Na yi wannan domin dukan waɗanda suke daga wannan bangon duniya zuwa wancanSu sani ni ne Ubangiji,Ba kuwa wani Allah sai ni.

7. Ni na halicci haske duk da duhu,Ni ne na kawo albarka duk da la'ana.Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.

8. Zan aiko da nasara daga sararin sama kamar ruwan sama.Ƙasa za ta buɗe ta karɓe ta,Za ta kuwa hudo da 'yanci da gaskiya.Ni Ubangiji, ni zan sa haka ya faru.”

9. Ko tukunyar yumɓu tana iya gardama da magininta,Tukunyar da take daidai da sauran tukwane?Ko yumɓu ya iya tambayar abin da maginin yake yi?Ko tukunya tana iya gunaguni a kan magininta?

10. Ko akwai wanda zai iya ce wa iyayensa,“Don me kuka haife ni kamar haka?”

Karanta cikakken babi Ish 45