Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 42:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Zan lalatar da tuddai da duwatsu,In kuma busar da ciyawa da itatuwa,Zan mai da kwaruruka inda akwai rafi hamada,In kuma busar da kududdufan ruwa.

16. “Zan yi wa mutanena makafi jagoraA hanyar da ba su taɓa bi ba.Zan sa duhunsu ya zama haske,In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu.Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.

17. Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka,Masu kiran siffofi allolinsu,Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”

18. Ubangiji ya ce,“Ku kasa kunne, ya ku kurame!Ku duba da kyau sosai, ku makafi!

19. Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta,Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?

20. Isra'ila, kun ga abu da yawa,Amma bai zama da ma'ana a gare ku ba ko kaɗan.Kuna da kunnuwan da za ku ji,Amma a ainihi me kuka ji?”

21. Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa,Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,

22. Amma yanzu an washe mutanensa,Aka kukkulle su a kurkuku,Aka ɓoye su a rami.Aka yi musu fashi, aka washe su,Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.

23. Ko akwai wanda zai kasa kunne ga wannan?Ko za ku kasa kunne ku yi lura daga yanzu?

24. Wane ne ya ba da Isra'ila ga masu waso?Ubangiji ne kansa, shi wanda muka yi wa zunubi!Ba mu iya zama kamar yadda yake so mu yi ba,Ko mu yi biyayya da koyarwarsa da ya ba mu.

25. Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa,Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo.Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra'ila kamar wuta,Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba,Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.

Karanta cikakken babi Ish 42